News
An Yi Karon Batta Tsakanin Makiyaya Da Manoma A Kwara
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Rashin fahimtar juna da ya janyo sa’insa kan hakkin mallakar filayen kiwon dabbobi ya auku tsakanin makiyaya da manoma, inda ya kai ga an zubar da jini a Jihar Kwara.
A cewar mai magana da yawun Hukumar Tsaro da Civil Defence a Jihar Kwara, Babawale Zaid Afolabi, ya je sa’insar ce ta kai ga an yi amfani da adduna da sauran makamai a yayin da bangarorin biyu suka hau dokin zuciya.
gonaki da burtalan kiwo ba kan shi farau ba.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da neman mafitar rikicin makiyaya da manoma, inda hankali ya fi karkata a zuciyar mahukuntan Najeriya na kare tsarin kiwon gargajiyar shekaru aru-aru a kasar.