News
Gobara ta kashe uwa da jariri ta a Kano
Daga kabiru basiru fulatan
Gobara ta yi sanadiyar rasa ran wata mata, Zainab Yusha’u da jaririnta ɗan shekarar 1, Sulaiman Usaini a Kano.
Gobarar ta ƙone gidan nasu ne da ke kan titin Gwarzo, kusa da gidan kaji.
Kakakin Rundunar Ƴan Kwana-kwana ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwa lamarin.
“A yau, 8 ga watan Janairu mun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 7 na safe da ga wani Usman Nura inda ya sanar da mu cewa gobara ta tashi a gidan.
“Sai mu ka garzaya mu ka je wajen da misalin ƙarfe 7:8 na safe. Ko da mu ka je sai mu ka tarar da gobarar.
“Mun samu mutum biyu, Zainab Yusha’u da jaririnta Sulaiman Usaini sun makale a gidan.
“Bayan nan sai muka ceto su, amma ina rai yayi halinsa kuma tuni mu ka mikawa mijin marigayiyar gawar ta da ta jaririn ,” in ji Abdullahi.