News
“Bazamu shimfida muku gadar sama da ta kasa a banza ba” – Ganduje ga ‘yan Adaidaita-sahu

Daga kabiru basiru fulatan
“Bazamu shimfida muku gadar sama da ta kasa a banza ba” – Ganduje ga ‘yan Adaidaita-sahu
“Kullum sai an karbi kuɗaɗe a hannun mu kuma ba ma ganin amfanin kuɗin da mu ke biya,” in ji wani direban adaidaita-sahu
Gwamnatin Jahar Kano bisa jagoranci na Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a kwanakin baya tace duk irin aikace-aikacen da takeyi na gyaran tituna sabbi da tsofaffi ga kuma shimfida gadoji sama da kasa ga tallafin da take bayarwa ga masu baburan duk ba zasu tashi a banza ba.
Gwamnan ya bayyan hakane yayin da ‘yan Adaidaita-sahu suke korafin sanya musu wata daira 100 a kullum.
A yanzu haka dai ‘yan baburan sun tsunduma Yajin aiki biyo bayan yadda hukumar KAROTA ta ce sai sun biya kudi Naira 8,000 domin sabunta lambar su.