Connect with us

News

Gwamnatin Buhari ta tabbatar da kisan gillar mutane 200 a cikin mako guda a Zamfara

Published

on

FB IMG 16418117167953338
Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

 

 

Advertisement

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane akalla 200 tare da raba dubbai da gurin zamansu, a wasu munanan hare-hare da aka kai a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin kasar a makon jiya.

A ranar Asabar din da ta gabata wasu mazauna yankunan da lamarin ya shafa sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 140 tsakanin Laraba da Alhamis.

Ministar agajin jin kai, Sadiya Umar Farouq, ta tabbatar da adadin wadanda suka mutu a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta Nneka Ikem Anibeze ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata, inda ta kara da cewa sama da mutane 10,000 ne ‘yan ta’adda suka raba da matsugunansu tare da kona su a wasu kauyukan Bukuyyum da Anka. Karamar Hukumar Jahar Zamfara.

Advertisement

Duk da cewa gwamnatin jihar Zamfara ta musanta zargin, amma ta ce adadin wadanda suka mutu ya kai 58, bayan Sarkin Anka ya ce an kashe mutane 22 a yankinsa, yayin da Sarkin Bukkuyum ya sanar da mutuwar wasu 36, kamar yadda kakakin gwamnatin jihar Zamfara ya bayyana. Zailani Bappa. ya tabbatar a cikin wata sanarwa da aka fitar a yammacin ranar Asabar.

Bayanai sun ce daruruwan ‘yan ta’addan da suka kai munanan hare-haren suna biyayya ga fitaccen dan fashin nan mai suna Bello Turji, wanda jiragen yakin Najeriya suka tilastawa barin sansaninsu da ke dajin Fakai. Karamar Hukumar Shinkafi.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *