Connect with us

News

Ministar jin kai, Sadiya Umar Farouq ta yi Allah-wadai da kashe-kashen da ake yi a jihar Zamfara

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

Sadiya Umar Farouq ta yi Allah-wadai da kashe-kashen da aka yi a Jihar Zamfara, inda ta bayyana ‘yan fashin a matsayin abin tsoro.

Ministar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun mai taimaka mata na musamman kan harkokin yada labarai, Nneka Ikem Anibeze, ta bayyana hakan ne biyo bayan farmakin da aka kai wasu kauyuka biyar tare da kashe sama da mutane 200 a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum na jihar.

“Wannan abin tsoro ne kuma abin takaici. Sama da mutane 200 ne aka yi jana’iza sakamakon mamayar da ‘yan fashi suka yi.

Advertisement

“Mun yi matukar bakin ciki da wannan farmaki da kashe-kashen da ‘yan bindiga ke yi, kuma mun damu da ’yan gudun hijirar da ke gudun hijira da daruruwansu daga yankunansu, musamman mata da yara.

“Muna jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Zamfara a wannan lokaci, muna kuma jajantawa iyalan wadanda suka mutu. Muna addu’ar Allah ya jikan su ya kuma dawo mana da zaman lafiya cikin gaggawa”.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *