News
Rikicin APC a Kebbi: Ku buɗe ofisoshin jam’iya a kowacce ƙaramar hukuma, Aliero ya umarci mabiya
Daga Muhammad zahraddin
Adamu Aliero, jagoran wani ɓangare na Jam’iyar APC a Jihar Kebbi, ya umarci mabiyansa da su buɗe ofishin jam’iya a kowacce da ga ƙananan hukumomi 21 na jihar.
Aliero, Sanata mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya, ya bada wannan umarni ne lokacin da ɗumbin magoya bayansa su ka tarbe shi a Filin Sukuwa a Birnin Kebbi.
Da ya ke jawabi ga mabiyan nasa, Aliero ya ce “ba za mu yadda da kama-karya wajen naɗa shugabannin jam’iya ba.”
Ya ce ɓangaren sa na APC ya ɗauki gaɓaran buɗe ofisoshi na adawa ne domin ya yaƙi rashin adalcin da a ka yi wa wasu yan jam’iyyar na cire su ta ƙarfi da yaji da ga muƙaman su na shugabancin jam’iya a jihar.
Sanatan ya yi zargin cewa waɗanda a ka cire a zaɓen shugabacin jam’iyar, an maye gurbin su da wasu ne kawai saboda su na goyon bayan sa.
Sabo da haka, Aliero ya ci alwashin samun nasara a jam’iyar da kuma ci gaba da yaƙi da rashin gaskiya.
Sai dai kuma da a ka tuntuɓe shi ta wayar salula yau Litinin, Shugaban APC a jihar, Abubakar Kana-Zuru ya ce bashi da wata masaniya ta rabuwar jam’iya a jihar.
Ya ƙara da cewa an yi zaɓen shugabannin jam’iya na jiha a bisa kan doron sharudda da matakai da uwar jam’iya ta zaiyana.