Connect with us

News

Ƴan sanda sun cafke matashin da yai garkuwa da ƴar shekara 13 ya kuma hallaka ta a Kano

Published

on

IMG 20220112 WA0009
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kano ta sanar da cafke wani matashi mai suna Auwalu Abdulrashid da ya yi garkuwa da wata yarinya ƴar kimanin shekara 13, mai suna Zuwaira ya kuma kashe ta.

Rundunar ta ce a na tunanin sabo da ya fahimci yarinyar ta gane shi, shine ya kashe ta sabo da ka da ta tona masa asiri.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata da daddare.

Advertisement

Ya ce a ranar 21 ga watan Yuni, 2021 su ka samu rahoto da ga wani mazaunin garin Tofa, da ke Ƙaramar Hukumar Tofa a Jihar Kano cewa an yi garkuwa da ƴarsa mai suna Zuwaira, mai shekaru 13 tare da buƙatar ya bada kuɗin fansa har naira miliyan daya.

Ya ce da ga baya ne kuma a ka daidaita a kan Naira dubu ɗari huɗu, in da yayin da ake tattaunawa don biyan kuɗin fansar, a ka gano gawar yarinyar a wani kango inda aka yanka ta kuma a ka binne a wajen.

” Bayan samun wannan mummunan rahoton, an ziyarci wurin, aka tono gawar, likitoci kuma su ka tabbatar da mutuwarta, inda muka mika gawar ga ’yan uwanta don a yi mata jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada”. Inji Kiyawa.

Advertisement

Sanarwar ta ce hakan ya sa Kwamishinan Ƴan Sanda na Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya umarci rundunar ‘Operation Puff Adder’, karkashin jagorancin SP Shehu Dahiru da su bazama neman wanda ya aikata laifin.

Kiyawa ya ci gaba da cewa haka jami’an su ka tsunduma neman mai laifin har tsawon kwanaki 202, sannan su ka samu nasarar kama Abdulrashid, wanda ake kira da Lauje, ɗan kimanin shekaru 21 a garin Tofa a ranar 9 ga watan Janairu, 2022.

DSP Kiyawa ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya amsa cewa, shi kaɗai ne ya yi garkuwa da yarinyar ya kuma kashe ta.

Advertisement

Sannan Kiyawa ya ƙara da cewa, a 07/06/2021, Abdulrashid ya kuma yi garkuwa da ƙanin ita wannan yarinya da ya kashe, mai suna Muttaka, mai shekaru 3 a garin Tofa, inda ya buƙaci a biya shi kuɗin fansa naira miliyan biyu, daga baya ya dawo Naira dubu ɗari, inda da ga bisani ya jefar da yaron a makarantar firamare ta Dawanau.

A sanarwar, Kiyawa ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin girbar abin da ya shuka.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *