News
An dage shari’ar da a ka shigar da gwamnati a kan dakatar da Twitter
Daga Yasir sani Abdullah
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Legas ta dage sauraron karar da lauyan kare hakkin dan Adam, Inibehe Effiong ya shigar zuwa ranar 18 ga watan Maris.
Lauyan ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba.
Sauraron zaman da a ka yi yau a Legas an dage zaman ne yayin da mai shari’a A. O. Faji na babbar kotun tarayya zuwa ranar da aka ce.
Ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, “A yau ne babbar kotun tarayya da ke Legas ta gabatar da kara a kan Ministany yada labarai da gwamnatin tarayya a watan Yunin bara domin kalubalantar dakatar da Twitter a Najeriya.
SaharaReporters ta rawaito yadda gwamnatin Najeriya a watan Yunin 2021 ta dakatar da Twitter, ta na mai cewa, ta na barazana ga kamfanoninta.
An dakatar da dandalin ne bayan da Twitter ya goge wata sanarwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter, wanda da yawa daga cikin ‘yan Najeriya suka nuna rashin jin dadi.Bayan haka Effiong ya maka ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed da Abubakar Malami, da gwamnatin tarayya kara a kan dakatar da dandalin sada zumunta.