Connect with us

News

YANZU-YANZU: APC ta dakatar da babban taron kasa

Published

on

Spread the love

Daga Usman Abdullah jibirin

 

 

Advertisement

An dage babban taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da za a yi a watan Fabrairu zuwa watan Yuni.

Rahotonni sun tabbatar da cewa shugabannin jam’iyyar da kwamitin tsare-tsare na rikon kwarya (CECPC) sun yi tasiri wajen dakatar da taron saboda karafe-korafe da suka taso daga wasu jahohin da jam’iyyar ke mulki, kananan hukumomi, da na mazabun jihohi, da kuma wasu bangarori duk ana fuskantar rashin jituwa.

A baya an zargi kwamitin Gwamna Mai Mala Buni bai da niyyar shirya zaben shugabannin jam’iyyar APC Mai Mala Buni ya samu goyon bayan wasu Gwamnonin APC da Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN

Advertisement

Akwai alamun da ke nuna cewa shugaban kwamitin rikon kwarya na APC, Mai Mala Buni yana kokarin dakatar da zaben shugabannin jam’iyya.

Sunce Gwamnan ya shantake a kujerar shugaban APC na kasa, har ya fara hangen mataimakin shugaban kasa

Punch ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 12 ga watan Junairu, 2022 cewa Mai Mala Buni yana da goyon bayan gwamnoni; Atiku Bagudu da Badaru Abubakar.

Advertisement

Ana kuma zargin cewa Ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami yana cikin wadanda ke marawa kwamitin Mala Buni baya don a daga zaben da za ayi.

Jaridar tace ana tunanin Mala Buni na neman dabarar da zai yi ya cigaba da zama a kan kujerar shugaban jam’iyya har su fitar da ‘dan takarar shugaban kasa.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *