News
Za’a Yi Kidayar ‘yan Kasa a Watan Mayu
Daga Yasir sani Abdullah
Za a yin kidayar ‘yan kasa a watan Mayu mai zuwa, bayan shekara 15 da aka taba yin kidayar, a cewar shugaban hukumar kidaya ta Nijeriya National Population Commission.
Shugaban Hukumar, Nasir Isa Kwarra ya ce fasahar zamani za ta taimaka wajen tabbatar da cewa an gudanar da sahihiyar kidaya da ake sa ran za a gudanar a watan Mayu mai zuwa.
Wasu ‘yan kungiyoyin kudancin Nijeriya ba su yarda da sakamakon kidayar da aka yi ba a shekarar 2006, suna masu zargin magudi don fifita yankin arewacin Nijeriya.
Kiyasi ya nuna cewa al’ummar Nijeriya sun kai miliyan 200, idan aka kwatanta da miliyan 140 da aka samu a shekarar 2006.