News
An kama Janar ɗin bogi da almundahanar N270m bayan yai ƙaryar cewa Buhari zai naɗa shi Shugaban sojin ƙasa
Daga Usman Abdullah jibirin
Jami’an Yankin Legas na Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa, EFCC sun cafke wani Janar ɗin sojin ƙasa na ƙarya, Bolarinwa Oluwasegun, a kan zargin almunhanar naira miliyan 270.
Oluwasegun, wanda yai ƙaryar cewa shi mai muƙamin Janar ɗin sojojin ƙasa ne, ya yankawa Kodef Clearing Resources ƙaryar cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya fitar da sunan sa, shi da wani, cewa zai naɗa shi muƙamin Shugaban Rundunar Sojojin Ƙasa, shi yasa ya ke neman ƴan kuɗaɗe domin ya shiga ya fita a bashi muƙamin.
Haka-zalika, wanda a ke zargin ya bugo shaidar ɗaukar aiki ta ƙarya, ɗauke da sa hannun Shugaban ƙasa na ƙarya ya nunawa kamfanin da ya karɓi kuɗaɗen a wajen sa.
Da ga bisani me da Kamfanin ya gano cewa ƙarya ne, sai ya kai ƙarar shi ofishin EFCC.