Opinion
HAƊIN KANMU SHI NE MAFITA A GAREMU
Daga rabi,u mustapha
Ya kamata matasa da sauran jama’a mu haɗa kanmu don kawo canji a zaɓe mai zuwa.
Abin da ya kamata matasa da sauran jama’ar gari mu yi shi ne mu ajiye duk wata adawa ta siyasa da cece-kuce mu haɗa kanmu mu zaɓi cancanta ba jam’iyya ba.
A halin da mu ke ciki a ƙasar nan ba mu da lokaci na gaba, adawa, da faɗa na siyasa, babban abin da ya kamace mu yi shi ne jajircewa da kuma samar da haɗin kai sannan mu duba cancanta da abinda zai zama mafita a garemu!
Akwai hanyoyi da dama da za mu bi wajen kawo canji da cigaba a yankin mu tare da dawo da martabar ƙasarmu.
Sai mun samar da haɗin kai tsakaninmu sannan zamu san mu su waye ko suwa zamu zaɓa a matsayin shuwagabanni da kuma sanin matsalar ƙasarmu da samar da hanyoyin magance matsalar.
Sannan samar da haɗin kan zai wanzar da zaman lafiya tare da rage rashin aikin yi da matasanmu ke fama da shi. Matasa za su san kansu su daina shaye-shaye da jagaliyar siyasa.
Ina kira ga ɗaukacin ƴan ƙasarmu mai albarka da mu dawo daga rakiyar rigingimu na siyasa wanda bazai haifa mana ɗa mai ido ba face kashe-kashe, ta’addanci, tada zaune tsaye, rugurguza tarbiyya da rayuwa ta matasan mu.
Abin da ya fi kamata shi ne mu koma ga Allah mu sasanta kanmu, mu zama ɗaya sai mu zauna lafiya cikin aminci kuma zamu ceto ƙasarmu daga halin da take ciki domin kwanciyar hankalin ƙasarmu shi ne kwanciyar hankalinmu.
Allah Ya sa mu dace.