News
Ɗan makaranta ya harbe ɗan ajinsu kafin ya kashe kansa

Daga Usman Abdullahi jibiri Ngurun Yobe
Wani ɗan makaranta mai shekara 16 a Afirka ta Kudu ya harbe ɗan ajinsu biyo bayan wata rigima tsakaninsu, inda daga baya ya kashe kan sa.
Yaran suna mataki na 10 a Sakandaren Lesiba da ke Daveyton.
Hukumomi sun ce an yi harbin ne ranar Laraba yayin da aka koma sabon zangon karatu.
‘Yan sanda na gudanar da bincike kan lamarin kuma an tura jami’an kula da lalurar ƙwaƙwalwa da zimmar duba lafiyar waɗanda abin ya ritsa da su.