News
Mazauna Legas na shan buhu 100 na wiwi a kullum — Bincike

Daga kabiru basiru fulatan
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA, ta baiyana cewa a na shan wiwi buhu 100 a rana a Jihar Legas.
Wannan na ƙunshe ne a wani bincike da Kamfanin Daillancin Labarai na ƙasa NAN ya saki a yau Juma’a.
A binciken, NAN ta tattauna da Lauyan rundunar NDLEA ta Legas, Jeremiah Aernan, wanda ya nuna damuwa da yadda matasa ke shan miyagun ƙwayoyi ba ƙaƙƙautawa.
Aernan ya nuna cewa kafar sadarwa ta zamani ce ummul-aba-isin wannan ta’ada ta shaye-shaye tsakanin matasa.
“Yanzu fa a kafar sadarwa a ke rarraba miyagun ƙwayoyi. Abun ma ya zama ta nan a ke cinikayyar sa.
“Da matashi ya ji yana da buƙata, kawai zai sa oda ne ta yanar gizo, kamar yadda a ke sa oda a sayi sauran kayayyaki ta yanar gizo.
A cewar Aernan, abokai ma su na taka rawa wajen shaye-shaye, wanda a cewar sa, yana sanya wasu matasan su shiga ƙungiyoyin ƴan asiri.
Ya baiyana cewa ƙididdiga ta nuna cewa a rana a na shan tabar wiwi sama da buhu dari a Legas.
“idan ka bincika yawan ranar wiwi da a ke sha a kullum a Legas, za ka samu ce sun haura buhu dari.
“Mutum ne me siyar da wiwi ya na samun ribar Naira dubu 3 a rana, ya zai ai ya dena wannan harkar?,” In ji Aernan.
Ya yi kira ga a haɗa hannu guda wajen yaƙar wannan mummunar ta’ada a jihar da ma ƙasa baki daya.