News
Tinubu ya bada tallafin N50m ga waɗanda harin ƴan ta’adda ya shafa a Zamfara

Daga kabiru basiru fulatan
Jagoran Jami’yar APC na Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a jiya Alhamis ya bada tallafin naira miliyan 50 ga ƙauyukan da hare-haren ƴan ta’adda ya shafa a kwanan nan a Jihar Zamfara.
Tinubu ya sanar da bada tallafin ne jim kaɗan bayan ya kaiwa Gwamna Bello Matawalle ziyarar jaje a Gusau.
Tinubu, tsohon Gwamnan Jihar Legas, ya yi kira da a dage da addu’a domin kawo ƙarshen rashin tsaro a jihar.
“Zan iya yiwa mutanen jihar nan addu’a da ga ko ina na ke, amma zuwan nawa ya fi muhimmanci.
“In dai a ka haɗa hannu guri guda, to za a kawo ƙarshen maƙiyan ilimi, Boko Haram da sauran ƴan ta’adda.
“Mu addu’a mu ke ta yi kan Allah Ya kawo mana zaman lafiya a gaba ɗaya ƙasar nan. Amma idan maƙiyan nan namu su ka ƙi daina wa, to fa za mu ƙarar da su.
“Mu mun amince da ƙoƙarin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wajen wanzar da zaman lafiya, doka da oda da kuma dawo da ƙasar nan kan ƙadamin tattalin arziki da ci gaba,” in ji Tinubu.
A na shi jawabin, Matawalle ya ce ziyarar ta Tinubu za ta sauƙaƙa raɗaɗin hare-haren a zukatan waɗanda abin ya shafa.
Ya kuma godewa Tinubu a bisa tattakin da ya yi ya kawo ziyarar jaje a jihar.