‘Yan wasan na Super Eagles sun doke Sudan da ci 3-1 inda Samuel Chukwueze ya yi sammakon zura kwallon farko a minti na uku da fara wasa.
Kwallo ta biyu kuma ta zo ne daga Taiwo Awoniyi gab da za a tafi hutun rabin lokaci, wato a minti na 45.
Bayan kuma da aka dawo daga hutun rabin lokacin ne Moses Simon shi ma ya ba da tashi gudunmowar kwallon a minti na 46.
Sai dai a minti na 70 Sudan ta samu bugun fenariti wacce Khedr Safour Daiyeen ya buga ya ci.
Duk da cewa sun zubar da dama da yawa a karawar, Najeriya ta yi hobbasan ganin ta mallaki gurbi a zagayen da za a fara sallamar kasashe zuwa gida.
Najeriya ta lallasa Masar a wasanta na farko inda ta doke tawagar dan wasan Liverpool Mohamed Salah da ci daya mai ban haushi.
Sau uku Najeriya tana lashe kofin na AFCON, lokaci na baya-bayan nan shi ne a shekarar 2013.
Ita kuwa Sudan ta taba lashe kofin gasar a shekarar 1970 kuma shekararta goma rabon da ta halarci gasar ta AFCON sai a wannan karo.
A wasanta na farko, Sudan ta tashi kunnen doki da Guinea-Bissau a wasanta na farko inda har golanta Ali Abu Achrine ya yi nasarar kakkabe wani bugun fenarti.
A ranar Laraba Najeriya za ta kara da Guinea-Bissau duk da cewa ta shiga zagaye na gaba yayin da Sudan za ta fafata da Masar.