Sports
Australia zata Kori Novak Djokovic daga kasarta
Babban mai shari’a a kasar Ostiraliya James Allsop ya ce hukuncin kotun tarayya ya ta’allaka ne a kan halaccin matakin da hukumar shige da ficen kasar ta dauka da kuma dalilai uku na daukaka kara da lauyoyin Djokovic suka shigar.
Dan wasan tennis na duniya Djokovic mai shekaru 34, ya daukaka kara a kotu bayan da Shugabar hukumar shige da fice na Ostiraliya Alex Hawke ya yi amfani da ikonsa wajen soke bizar dan wasan bisa hujjar cewa zai zama bazana ga lafiyar jama’a saboda rashin yin rigakafin corona, hukumar ta kuma stare dan wasan a wani otel na musamman a ranar 6 ga watan Janairu.
Yanzu haka dai Djokovic ba zai sami damar kare kambunsa a karo na goma ba a gasar Australian Open da za a fara ranar Litinin a birnin Melbourne na kasar Ostiraliya.