Sports
Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Navas, Van de Beek, Kurzawa, Dembele, Vlahovic, Tielemans, Carroll
Daga muhammad muhammad zahraddin
Newcastle United na shirin aikawa da tayi kan golan Paris St-Germain Keylor Navas, sai dai kungiyar ta Faransa na son dan wasan mai shekara 35 dan kasar Costa Rica ya yi zamansa. (RMC Sport via Mail)
Dan wasan tsakiya na Manchester United Donny van de Beek mai shekara 24 ya yi watsi da tayin komawa Newcastle saboda matsayinta na baya-baya da take kai a teburin Firimiyar Ingila. (Telegraph – subscription required)
Newcaste din dai na kara samun nasara a kokarin da suke yi don dauko Diego Carlos, dan wasan Sevilla mai shekara 28. (Express)
Chelsea na son daukan Layvin Kurzawa dan wasan baya na Paris St-Germain mai shekara 29 amma a matsayin na aro. (Fabrizio Romano on Twitter)
Southhampton na tattaunawa da Chelsea kan sayen Armando Broja dan kasan Albania mai shekara 20. (Guardian)
Dan wasan gaban Barcelona, Ousmane Dembele na iya komawa Manchester United ko Juventus ko Chelsea amma da alama Bayern Munichce ba ta da damar samun dan wasan mai shekara 24. (Sport – in Spanish)
Leicester City na shirin rabuwa da Youri Tielemans, dan wasan tsakiya mai shekara 24. (Mirror)
Arsenal na son daukan Tielemans wanda ke da sauran wata 18 a kwantiraginsa da Liecester. (Sun)