Mai masaukin baƙi Kamaru ta kammala wasannin rukuni na A a mataki na ɗaya biyo bayan 1-1 da suka tashi da Cape Verde a birnin Yaounde a gasar Kofin Ƙasashen Afirka.
Vincent Aboubakar ne ya ci wa Kamaru ƙwallo da ƙafar hagu a minti na 39 da take wasa.
Sai kuma a minti na 53 Rodrigues ya farke inda ya saka ƙwallo a raga mai ƙayatarwa da gefen ƙafarsa bayan Rocha Santos ya bugo masa ita daga gefen dama.
Rabon da a doke Kamaru a birnin Yaounde tun 1988, kuma wannan nasarar ta sa za su ci gaba da kasancewa a birnin don buga wasan zagayen ‘yan 16 da wadda za ta fito daga rukunin C ko D ko E a matsayin ta uku.
Za a fara buga wasan zagayen ranar Litinin, 24 ga Janairu.