News
Mawakan wakokin Ingausa sun yi waka kan kwarafshan
Mawakan wakokin Ingausa sun yi waka kan kwarafshan
Marubuta wakokin hausa da na Turanci a Najeriya sun koka dangane da yadda cin hancin da rashawa ya dabai baye kasar.
Marubutan dai na wannan koke ne cikin wasu wakoki gwama Hausa da turanci da suka rubuta aka kum attatarasu cikin wani littafi da suka yiwa lakabi da ‘Kwarafshan’.
Taron wanda ya sami halartar mallaman jami’o’I da banagren yaki da cin hancin da rashawa a Najeriya, da Matasa, ya mayar da hankali kan yadda za’ai amfani wakar Ingausa wajen jan hankalin matasan kasar cin yaki da cin hanci da rashwa da kasar ke yi.
Wakilin BBC a Kano da ya halarci taron, ya rawaito cewa shugaban kungiyar marubuta wankokin hausa da na turanci a Kano Khalid Imam shi ne ya jagoranci taron, ya kuma ce shi ne karon farko da aka tattara wakokin wuri guda.
”Mun yi wannan littafi da aka sanyawa suna Kwarafshan, domin mu fadakar da jama’a illolin da cin hanci da rashawa ya ke da shi, da rusa kasa da ya ke yi, ta yi wa kasa tarnaki wajen ci gaba. Fatan mu a karshen taron nan shi ne jama’a su san cewa maganar yaki da cin hanci da rashawa ba nauyin gwamnati ne kadai ba, alhakin kawo gyaran ya rataya a wuyan al’umma. Ni da kai, da ke da ku dukka mu na da rawar da za mu taka domin ganin mun yaki cin ha nci da rashawar,” in ji Imam.Wasu daga cikin jagororin taron irinsu farfesa Sadik Isa Radda, shugaban kwamitin gwamnatin Najeriya wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar, na da ra’ayin cewar amfani da wakokin ingausa wajen yakar cin hanci da rashawa zai yi tasiri wajen cusawa irin wadannan matasa akidar kaucewa munanan dabi’un da ka iya janyo aikata rashawa.
Radda ya kara da cewa gwagwarmayar da gwamnati ke yi don yaki da rashawa ya samu karbuwa ga matasa, shi ya saakon da gwamnati ke ba da wa ya ke zuwa kunnensu, kuma a yanzu sun maida lamarin mai muhimmanci ta hanyar sanya shi cikin wake, da rubuce-rubuce domin fadakarwa.
”Abin farin ciki anan shi ne, wadanda sukai wadannan wakoki matasa na tsakanin shekara 20 zuwa 25, hakan na nufin tun yanzu za su fara kyamatar abin, sannan za su yada kyamar abin ga sauran al’umma ta hanyar amfanbi da bai war da Allah ya yi musu,” in ji Radda.
Suma wasu daga cikin matasan da suka gabatar da wakoki a kan cin hancin da rashawar sun bayyana cewa za su yi duk kokarin domin ganin sakon ya isa ga wadanda aka yi dominsu, wato matasa ‘yan uwansu.