Connect with us

Uncategorized

RAHOTO NA MUSAMMAN KAN CUTAR SIKILA KO AMOSANIN JINI

Published

on

FB IMG 16424081887911645
Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

 

 

Advertisement

Cutar sikila ko amosanin jini na daya daga cikin cututtukan da za a iya cewa na neman zama ruwan dare.

Larurar amosanin jini, wato sickle cell anaemia, mugun ciwo ne. Larura ce da ke raunatama da ita har ma da iyalan mai fama da ita, da al’umma baki daya.

Awani bincike da kungiya kiwan lafiya ta majalisar dankin Duniya ta fitar wato (WHO) tabayyana cewa,
Najeriya itace ƙasar da tafi kowace ƙasa yawan masu cutar a duniya. Binciken ya nuna cewa duk shekara ana haifar jarirai 300,000 masu ɗauke da wannan cuta a faɗin duniya, amma rabi daga Najeriya ake haifar su. Daga cikin 150,000 da ake haifa a Najeriya ɗin, kusan 100,000 ne suke mutuwa a duk shekara.

Advertisement

Alƙaluman ƙididdiga sun nuna cewa ma fi yawan masu wannan cuta ta sikila ko amosanin jini da ake haihuwa a Najeriya suna Arewacin ƙasar ne. Masana kiwon lafiya sun yi amanna cewa rashin yin gwajin jini kafin aure yana taka muhimmiyar rawa, wajen haifar yara masu ɗauke da wannan cuta ta sikila a wannan ƙasa tamu Najeriya.

saboda yadda ake yawan samun yin aure tsakanin masu rukunin jini AS da AS ko SS da AS dakuma SS da SS.

To kamar yadda tun a shekarun baya Gwamnatocin Jihohi da yawa suka tabbatar da dokar yin gwajin cutar ƙanjamau kafin aure, to ya kamata su sake tabbatar da dokar yin gwajin jinsin halitta (GENOTYPE) kafin aure, domin hakan zai daƙile yaɗuwar wannan cuta ta Sikila.

Advertisement

Tabbas akwai ƙarancin ilimantar da al’umma da kuma rashin wayar musu da kai akan sanin amfanin yin gwajin jinsin halitta (GENOTYPE) da rashin sanin ma’anar sa, da kuma sanin muhimmancin yin gwajin tun kafin soyayya tayi nisa har akai ga maganar aure, musamman a karkara da kauyuka.

Hakan ne yasa zan ta tattaunawa da wadanda suka cikaro da wannan larura bayan sunyi Aure batare da gwajin jinsin halittar ba wato (Genotype),

Bayan nan mun tin tibi wasu limaman Jihar Kano kan shi idan zasu Daura sure suna tambaya shedar gwajin jinsin halittar (Genotype)

Advertisement

Sa’annan muji daga bakin masu dauke da cutar da irin yadda sukeji.

Akarshe Mun tattauna da wani likita akan cutar da illolinta, da yawaitar ta ko kuma raguwar masu fama da ita, da hanyoyin kauce mata.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *