News
Ku harbe duk wanda ya yi yunkurin fasa gidan kaso’
Daga muhammad muhammad zahraddin
An bayar da wannan umarni ne da nufin shawo kan matsalar yawan hare-haren da ake kai wa gidajen yarin, al’amarin da wasu ke ganin kamar gwamnati ta gaza wajen kare wadannan wurare.
Wasu masana aikin na gidajen yarin a Najeriya, duk da sun yaba da wannan mataki, suna ganin ba a kan sa kadai ya kamata a tsaya ba.
Bisa ga dukkan alamu hukumomin Najeriya sun zuciya, kuma a yanzu a iya cewa sun yi kukan kura, dangane da batun hare-haren da ake yawan kai wa gidajen yarin kasar.
Inda mutanen da hukumomi ke kira bata-gari kan fasa gidajen kason, su yi kone-kone da sauran ta’adi a ciki, su kuma yi sanadin tserewar wadanda ke tsare a wadannan killatattun wurare na gyaran halayyar mutane.
Al’amarin da ya yi sanadin sulalewar mutum kusan dubu biyar daga gidajen a sassa daban-daban na kasar daga shekara ta 2020 zuwa shekara ta 2021. Yawancin su kuma har yanzu ba a kai ga sake cafke su ba.
A kokarin shawo kan wannan matsala ce, ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Ogbeni Rauf Are-gbe-sola ya ce tura ta kai bango, ya kuma bayar da kakkausan umarni ga ma’aikatan gidajen yarin kasar, a wata ziyarar aiki da ya kai gidan yarin Agodi da ke birnin Badun na jihar Oyo.
Yunkurin fasa wannan wuri da wani zai yi, hakan zai jawo kansa halaka ne kai tsaye, kar a bari mai irin wannan yunkuri ya rayu, har ya kai labari.
Inda duk wani ya yi kokarin fasa gidajen yari, to kar a raunata shi. Kar a harbe shi don a nakasa shi kawai. A harbe shi don a kashe shi. Muhimmin aiki na farko a nan shi ne, samar da ingantaccen tsaro,” in ji Are-gbe-sola.
To, ko ya kwararru a fannin aikin na gidajen yari ke kallon wannan umarni da gwamnantin Najeriya ta bayar? Wani tsohon babban jami’i a hukumar gidajen yarin Najeriyar, wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya shaidawa INDARANKA cewa
Masu lura da al’amura dai na yi wa wannan umarni kallon zakaran gwajin dafi, dangane da kokarin shawo kan matsalar ta fasa gidajen yarin Najeriya.