News
Matawalle ya ziyarci Buhari ya kuma ce kwanan nan ta’addanci zai zama tarihi a Zamfara
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ziyarci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a fadar sa da ke Abuja, inda ya bashi bayanin kan yanayin tsaro a jihar.
Da ya ke ganawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa, Matawalle ya ce kwanan nan za a daina ta’addanci a Zamfara kamar yadda ya samu tabbaci da ga Buhari.
A cewar sa, gwamnati ta samar da sabbin matakai da za a aiwatar da su wajen samar da dawwamammen zaman lafiya a jihar.
Matawalle ya ƙara da cewa duk sanda zai yi wani yunƙuri a kan rashin tsaro sai ya sanar da shugaban ƙasa kuma ya na samun goyon baya da ga gurin sa.
“Yau ma na zo da wata dabara kuma na sanar da shugaban ƙasa. Amma dai ba zan fadi dabarar a nan ba sabo da su lamura da su ka shafi tsaro, ba a so a riƙa baiyana su.
“Amma ina mai tabbatarwa jama’ar Zamfara cewa za su ga canji kwanan nan sabo da shugaban ƙasa ya da kwazon samar da zaman lafiya dawwamamme.
“Ina mai tabbatarwa da jama’a cewa mun da karfin da za mu magance wadannan mutanen,” in ji Matawalle.