News
Iran da Saudiya na gab da maido da alakar diflomasiya
Daga Yasir sani Abdullah
Jakadun Iran sun koma cikin Kungiyar Kasashen Musulunci mai shalkwata a Saudiya, a wani matakin farko na maido da alaka tsakanin kasashen biyu bayan sun katse huldar diflomasiyarsu a shekarar 2016.
Yanzu haka wakilan Iran sun isa birnin Jeddah na Saudiya domin fara aiki karkashin kungiyar ta kasashen Musulunci.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiya ta ce, wannan wani mataki ne da ke nuna cewa, kasashen biyu za su mayar da jami’ansu ofisoshin jakadancin kowanne daga cikinsu.
Kungiyar ta OIC ta ce, tawagar Iran din ta isa birnin Jeddah amma, kawo yanzu babu wani taro da ta halarta, kamar yadda wani jami’i a kungiyar ta Kasashen Musulunci ya shaida wa AFP.