News
IPOB: Gwamnatin Nijeriya ta sake tuhumar Nnamdi Kanu da sabbin laifuka
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
A jiya Litinin ne Gwamnatin Taraiya ta shigar da su sababbin laifuka da ta ke tuhumar Jagoran Haramtacciyar Kungiyar Rajin Samar da Biafara, IPOB, Nnamdi Kanu wanda yanke tsare a hannun gwamnati.
Ofishin Antoni-Janar na Ƙasa ne ya shigar da sabbin laifukan gaban Babbar Kotun Taraiya a Abuja, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Binta Nyako, inda a ka ƙara laifukan da ga bakwai zuwa 15.
Kanfanin Daillancin Labarai na ƙasa, NAN ya rawaito cewa, M. B. Abubakar, Daraktan Shigar da Ƙara, shine ya sanya hannu a takardar ƙarar mai lamb FHC/ABJ/CR/383/2015.
A ranar 19 ne dai a ke sa ran Kanu, wanda a ke zargi da laifuka bakwai na cin amanar ƙasa, zai sake fuskantar kotu a bisa wasu sabbin laifukan da su ka kai 15.
NAN ya rawaito cewa a ranar 2 ga watan Disamba, 2021 ne kotun ta sanya ranar Talata domin sauraron ƙorafe-ƙorafe da mai ƙara da wanda a ke ƙara su ka shigar gaban ta.
-
News4 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
News5 days ago
An Tura Kwamishinonin ’Yansanda 30 Da Jami’ai 15,000 Domin Sanya Ido A Zaɓen Osun
-
News7 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
