News
Gyaran Kundin Dokar Zaɓe: Majalisun Taraiya sun samu bambaci
Daga kabiru basiru fulatan
Majalisar Dattijai, a zaman ta na yau Laraba ta cire tsarin zaɓen fidda gwani na kai tsaye, wanda a ka fi sani da ƙato-bayan-ƙato.
Majalisar ta yi wa sashi na 84 kwaskwarima, in da ta maida shi cewa a zaɓen fidda gwani na jam’iya, za a iya yin ƙato-bayan-ƙato, ko naɗi, ko kuma yarjejeniya.
A tuna cewa a 2021 ne ta aikewa da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kundin gyaran dokar zaɓen, amma ya ƙi sanya hannu, in da ya ce sanya zaben ƙato-bayan-ƙato ya zama wajibi abu ne mai tsada, inda ya ƙara da cewa zai ɗorawa Nijeriya nauyi a tattalin arzikin ta da bai taka kara ya karya ba.
A ɗaya ɓangaren kuma, Majalisar Wakilai, a nata zaman na yau Laraba, ta sahale tsarin ƙato-bayan-ƙato da na naɗi, amma kuma ta cire tsarin yarjejeniya.
Sai dai kuma, da ga bisani sai ƴan majalisar su ka shiga ganawar sirri.