Opinion
Zaben Shugaba Nagari Yana Samar Da Kyakkyawan Shugabanci Ga Al’umma
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
A duk lokacin da al,ummarmu zasu zaɓi shugaba ya zama wajibi su duba da idon basira domin zaɓar shugaban da ba zasuyi nadama ba. Yana da kyau su duba chancantarshi ta zama shugaban a inda suke so ya shugabance su ta yin la’akari da wasu muhimman abubuwa tare da shi.
Abu mafi muhimmanci su duba waye shi? Shin yana da tarihi na taimakon al’umma a unguwarsu, ƙauyen su, garinsu ko yankin daya fito?
Tabbas Idan yana da kyakkyawar alaƙa tsakaninshi da al’ummarshi wannan Shine shugaban da ya dace su zaɓa sannan su cigaba da yi mashi addu,a tare da fatan alkhairi Allah ya taya shi riƙo domin yayi masu wakilci nagari. A duk lokacin da yayi kuskure kuma su makusantanshi su ji tsoron Allah su faɗa mashi gaskiya domin ya gyara.
Allah ya bamu ikon zaɓar shugabanni waɗanda suka cancanci shugabantar mu.