Opinion
Tabbas PDP ce za ta kafa mulkin Nijeriya a 2023 — Ayu

Daga Yasir sani Abdullah
Shugaban babbar Jami’yar adawa ta ƙasa, PDP, Iyorchia Ayu ya yi kira ga yan ƙasa da su ƙaunaci jam’iyar sabo da ita ce za ta samar da shugaban ƙasa a 2023.
Ayu ya bada tabbacin ne a ranar Lahadi a garin Fatakwal a wani biki da Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya haɗa.
A wata sanarwa da Mataimakin Wike kan Yaɗa Labarai, Kelvin Ebiri ya sanyawa hannu, Ayu ya nuna cewa dole a tashi tsaye a canja gwamnatin APC a 2023.
Ya zargi jam’iya mai mulki da gazawa wajen amfani da yawa da rabe-raben al’adu na ƴan Nijeriya ta sanar da al’umma ɗaya mai cike da ci gaba.
“Dole mu canja wannan tsari. Hanya daya ta canja wannan tsari shine mu goyawa PDP baya, wacce ita ce za ta samar da shugaba nan da shekarar 2023 a ƙasar nan,” in ji Ayu.
Ya kuma tabbatar da cewa Nijeriya za ta farfaɗo a hannun PDP, in da ya ƙara da cewa aikin farfaɗo da martabar kasar nan abu ne mai yiwuwa.
Ya kuma kara da cewa PDP za ta samar da shugabacin da zai haɗa kan ƴan ƙasa.