Hukumomin Burkina Faso sun ce sun toshe hanyoyin shiga shafin Facebook saboda tsaro.
Kakakin gwamnati Alkassoum Maiga ya ce ba lalle ba ne gwamnati ta yi bayani kan dalilin toshewar wadda aka fara gani ranar 10 ga watan Janairu, wadda kuma ta ci gaba.
Gidan rediyon Omega ya ruwaito kakakin yana cewa, ‘’ Ina ganin idan har muna da zabi tsakanin barin matsalar tsaro ta ta’azzara da kuma daukar matakin da zai iya ba mu damar takaita matsalar to ina ganin daukar matakin shi ne mafi dacewa domin amfanin kasarmu.’’
A ranar 11 ga watan Janairu, gwamnati ta sanar da cewa an kama wasu sojoji takwas bisa “shirin tayar da fitina”, abin da kafafen yada labarai na kasar suka ce yunkuri ne na juyin mulki.
Wata kungiyar tabbatar da ‘yancin amfani da intanet mai suna NetBlocks ta ce an samu katsewar intanet sosai a ranar 11 ga watan Janairu.
Kisan mutane 53 da ake zargin wasu masu ikirarin jihadi sun yi a watan Nuwamba da ya wuce ya janyo bacin ran yan kasa a kan gwamnati sakamakon kasa kawo karshen matsalar.
Tashin hankalin ya sa mutane kara fargabar yin juyin mulkin soja a kasar