Business
Albashi: Ma’aikatan simintin BUA sun yi zanga-zanga a Edo

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ma’aikatan kamfanin siminti na BUA da ke Obu-Okpella, Jihar Edo, sun rufe harkoki a masana’antar, bisa zargin rashin biyansu kudaden alawus-alawus da kamfanin ya yi.
Ma’aikatan da suka yi zanga-zangar, wadanda su ka tare kofar shiga kamfanin, sun rinka rera wakokin hadin kai tare da rike kwalaye a hannu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa zanga-zangar ta taso ne sakamakon samun labarin cewa, ma’aikatan kamfanin BUA bangaren siminti da ke Sokoto sun karbi alawus din su na hayar gidajen su na shekara, yayin da wadanda ke Okpella ba su samu komai ba.
An ce kamfanin na Sokoto ya hade da kamfanin Obu-Okpella tsawon shekaru biyu a fannin kula da yanayin ma’aikata.
Ma’aikatan da suka gudanar da zanga-zangar a ranar Laraba sun ce, suna kuma kokawa ne a kan yadda za a daidaita albashinsu da takwarorinsu na Sakkwato da kuma kawo karshen batun kwangila da ma’aikatan da ba su dace ba a Obu Plant.