Business
Manoman Tumatir na fargabar tashin sa a Kano
Daga Yasir sani Abdullah
Bayan rufe madatsar ruwa ta Tiga a jihar Kano, manoman Tumatur a jihar sun nuna fargabar cewa farashin tumatur na iya tashi a kakar bana, domin madatsar ruwan ita ce babbar hanyar samar da ruwan noman rani zuwa kananan hukumomi biyar na jihar da ke noman tumatur da kuma samar da tumatur.
A cewar manoman, rufewar wanda ya fara daga ranar 1 ga watan Nuwamba, kuma zai ci gaba har zuwa ranar 31 ga Maris, 2022, ya yi illa ga ayyukan noma a yankunan, inda suka ce an bar kadada mai yawa na fili ba tare da an kula da su ba saboda rashin ruwa.
Bayanai na nuni da cewa manoman tumatur da dama sun koma wasu wuraren da za su iya samun filaye kusa da wuraren ruwa don noman tumatur, yayin da wadanda suka samu gonakin noman ba su iya yin komai ba saboda rashin isasshen fili.
A nasa jawabin shugaban kungiyar masu noman Tumatir ta jihar Kano(TOGAN), Alhaji Sani Danladi Yadakwari, ya ce, manoman tumatur sun yi amfani da kasa da kashi 10 cikin 100 na filayen noman tumatur a wurin noman na Kadawa saboda madatsar rufewar madatsar ruwan. Ya yi nuni da cewa, manoman tumatur a jihar na cikin babbar matsala, wanda hakan zai haifar da karancin tumatur da hauhawar farashinsa.
“Saboda rufe madatsar ruwan, wasu daga cikin mambobinmu sun yi nasarar kawar da wasu yankuna da ke kusa da gabar kogin Kano don samar da tumatur, amma wannan bai kai kashi 10 cikin 100 na abin da muke yi a wurin noman Kadawa ba. Misali, a lokacin noman rani na bara, na noma kadada 15, amma a bana na iya noma kadada hudu kawai,”
Ya kara da cewa.”Har ila yau, wani mai sayar da Tumatir a Kasuwar ‘Yan Kaba da ke Jihar Kano, Mansur Bello Seemon, ya ce,TTumatur da ake samu a kasuwa a yanzu ya fito ne daga Zariya da ke Jihar Kaduna da kuma wasu sassan Jihar Katsina, yayin da tumatur da aka dasa a Jihar ya kasa kai wa. kasuwa. “A bara tumatur ya kasance ko’ina a wannan kasuwa, amma tun bayan rufe madatsar ruwa ta Tiga muke samun tumatur daga Katsina da Zariya. Yanzu ana siyar da kwando akan Naira 10,200 kuma dukkan alamu sun nuna cewa, tumatur zai yi tsada sosai a bana,” inji Seemon.
A halin da ake ciki, mahukuntan Hukumar Raya Kogin Hadejia Jama’are (HJRBDA) mai kula da madatsar ruwan sun bayyana cewa, an yanke shawarar rufe madatsar ne saboda, ta na bukatar gyara. Musamman jami’in hulda da jama’a na hukumar, Malam Salisu Baba Hamza, ya bayyana cewa gyaran ya yi daidai da shirin Transforming Irrigation Management in Nigeria (TRIMING) wanda bankin duniya ke daukar nauyin aiwatar da gyaran Kano. Shirin noman rani na kogin (KRIS) da kuma shirin noman rani na kwarin Hadejia (HVIS).
Ya kara da cewa kafin rufe madatsar ruwan, HJRBDA, kungiyoyin manoma, kungiyar masu amfani da ruwa (WUA) a jihar da kuma hukumar TRIMING sun yi taro inda suka amince da lokacin da za a rufe.