Entertainment
Jarumin Bollywood Ali Fazal ya yi Umrah

Daga Yasir sani Abdullah
Fitaccen jarumin fina-finan Bollywood na Indiya, Ali Fazal ya wallafa wani faifan bidiyo da ya nuna ya na aikin Umrah a dandalin sada zumunta na Instagram.
Tauraron ya rubuta cewa ya ziyarci Makka da Madina ne bayan kammala shirinsa na Hollywood mai suna Kandahar a Saudi Arebiya.
Ya ce ya sadaukar da Ummarar ga mahaifiyarsa – wacce ta mutu ranar 17 ga watan Yuni, 2020 da kuma kakansa.
“Zuwa Madina, sannan zuwa Makka!” Wannan hanya ce mai kyau ta kawo karshen ɗaukar fim dina!” Kamar yadda ya wallafa. “
“Na yi albarka sosai, ina tsammanin, ta hanyoyi da yawa. Ina son yin tunani a kalla.
“Wannan na Amma da Nana ne. Rashin su ba zai taba warkewa a zuciya ta ba… watakila waraka ba ita ce mafita ba. Bincike shine. Za mu gano. Amma na yi addu’a kuma na yi addu’a ga duk wanda ke kewaye da ni. Iyali, abokai da duk wanda ke buƙatar soyayya.
Ya kara da cewa akwai sauran abubuwan da mutane ke son bayarwa da karba. Ya ci gaba da kara da cewa ya “yi musu soyayya mai tsanani”.
Bidiyon ya samu gani daga miliyoyin masu amfani da manhajar.