Entertainment
Da 2.1 na gama jami’a, in ji Davido
Daga kabiru basiru fulatan
Fitaccen mawaƙin Nijeriya ɗin nan, David Adeleke, wanda a ka fi sani da Davido ya ce shi fa da sakamako mai daraja ta ɗaya, wato ‘Upper Second Class’ a turance ya kammala digirin sa a jami’a.
Davido, wanda mawakin Nijeriya ne mai alaƙa da mawaƙan Amurka, ya wallafa hakan ne a shafin sa na Twitter a jiya Talata.
A sakon danya wallafa, ya yi gargaɗi da a dena yin kuri da burga.
Ya ce “Abin mamaki!! Ni fa da 2.1 na gama jami’a. Amma ɗan baffa na, Dele, wanda daƙyar ya gama da 2.2, gashi nan ya na tashe “basira kenan”.
“Basirar da ba ta sanya ya tsinana komai a rayuwar sa ba.”
“Wannan rayuwar, taf!! “Mutanen Osun ku yi hattara da ƴan ƙarya,” in ji Davido.
NAN ya rawaito cewa a 2015 Davido ya kammala digirin sa a fannin kasuwanci a Jami’ar Babcock da ke Jihar Ogun.
A watan Disamba ne kuma ya sanar da cewa ya samu dala miliyan 22.3 a 2021.