Entertainment
Kayan kidan Hausawa na gargajiya da ke neman bacewa
Daga Yasir sani Abdullah
Hausawa sun shahara wajen amfani da kayan kade-kade da wake-wake na gargajiya.
Mawaka da makada kan yi amfani da wadannan kayan kida wajen isar da sakonninsu.
Akwai kayan kida daban-daban da Hausawa suke amfani da su wadanda suka hada da kalangu da ganga da goge da duma da sauransu.
Sai dai galibin matasa a yanzu ba su san wadannan kayan kida ko ma makada ba, kuma ma suna neman bacewa.