Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya haramta sayar da tarkacen tsoffin karafuna saboda yawaitar satar kayayyakin karafuna da ake yi a kasar.
An sanya dokar ne wadda ta fara aiki nan take saboda bannata muhimman kayayyakin gwamnati da ake yi domin a sayar da karafunansu.
Dokar za ta ci gaba da kasancewa har sai lokacin da gwamnati ta bullo da wani tsari na sanya ido kan yadda ake samo tsoffin karafunan da cinikinsu da kuma fitar da su daga kasar.
A makon da ya wuce ne Kenya ta samu kanta a cikin wani yanayi na rashin wutar lantarki a fadin kasar wanda ba ta taba shiga ba a ‘yan shekarun nan, inda binciken farko-farko ya danganta matsalar da bannata wayoyin manyan layukan lantarki a babban birnin kasar Nairobi.
An kama manyan jami’an kamfanin wutar lantarki na kasar ( Kenya Power and Lighting Company) aka gurfanar da su gaban shari’a a kan matsalar rashin wutar.
A yanzu ana ta samun karuwar matsalar bannata muhimman kayayyakin gwamnati da suka hada da layin dogo (kwangiri) da karafunan sabis din waya da kuma wayoyin wutar lantarki.
Shugaba Kenyatta ya ce bannata muhimman kayayyakin gwamnati laifi ne na cin amanar kasa, domin yana kassara tattalin arzikin kasa.
Wannan ba shi ne lokaci na farko da shugaban yake yin irin wannan gargadi ba.
Ko a lokacin da yake kaddamar da sabon layin dogo na zamani a 2017, Mista Kenyatta ya ce zai sanya hannu a zartar da hukuncin kisa a kan duk mutumin da aka kama da bannata titin jirgin kasan na biliyoyin dola, da aka yi aikinsa da kudin bashi daga China