Wata kotu da ke unguwar Kasuwan Nama a Jos, babban birnin jihar Filato a tsakiya Najeriya ta yi wa wani birkila hukuncin daurin shekara daya a gidan maza saboda samunsa da laifin satar kaza.
Alkalin kotun, Majistare Daniel Damulak ya zartar wa birkilan David Akubu mai shekara 17 hukuncin, bayan ya amsa laifinsa, amma kuma ya ba shi zabin biyan tara ta naira dubu goma.
Haka kuma ya umarci mai laifin da ya biya naira dubu biyar ga mai kazar, Madam Esther Dazam da ke unguwar Farin Gada, wadda ta kai shi kara, sannan ya guji aikata laifuka.
Tun da farko mai gabatar da kara, Mista Ibrahim Gokwat, ya sheda wa kotun cewa wanda aka gurfanar din ya saci kazar matar ne ya dafa ya kuma cinye tare da abokansa.