Connect with us

News

Buhari ya yi ta’aziyyar Hanifah, inda ya yabawa jami’an tsaro da suka kama wadanda ake zargi

Published

on

FB IMG 16428280826469037
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

ShugabanbanƘasaasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a ya jajanta wa Hanifah Abubakar, wata daliba ƴar shekara biyar da malaminta ya sace kuma a karshe ya kashe ta a Jihar Kano.

A wata sanarwa da Mataimaki na Musamman ga shugaban ƙasa a kan Yaɗa Labarai, Garba Shehu ya fitar, Buhari ya buƙaci hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar an yi adalci a kisan Hanifah.

Ya kuma umarci ƴan sanda da ma’aikatar shari’a da su tabbatar sun yi riƙo ingancin aikin binciken da ya haifar da kamo waɗanda a ke zargin ta hanyar yin shiri da kyau tare da gabatar da shari’a mai kyau da za ta ƙara ɗaga darajar kotu.

Advertisement

A cewar sanarwar, Buhari ya jajantawa ‘yan ƙasa da iyalan yarinyar a bisa ibtila’in da ya faru.

“Shugaba Buhari, ya yabawa ‘yan sanda da jami’an sirri kan yadda suka tona asirin bacewar Hanifa, musamman yadda aka kama malaminta da abokansa da a ke zargi da yin garkuwa da yarinyar da kuma kashe ta,” in ji sanarwar.

Buhari, a cikin sanarwar, ya lura cewa “iyali da daukacin al’ummar kasar da suka bi diddigin halin da Hanifa ke ciki a kullum tun bayan bacewarta suna fatan yarinyar ta dawo gida da rai da lafiya.

Advertisement

‘’Shugaban ya bayyana cewa kwazon binciken da jami’an tsaro su ka yi, wanda ya kai ga gano gawar ta tare da kame wadanda ake zargin wadanda tuni suka yi ikirari, abin yabawa ne.

Ya bayyana hakan a matsayin wata nasara da yakamata jama’a su kara yarda da hukuma, yana mai karawa da cewa, “idan aka samu irin wannan ci gaba, mutane za su rika magana daban-daban na tabbatar da doka.”

Sanarwar ta kara da cewa, ”Shugaba Buhari ya yi addu’ar Allah ya jikan wannan karamar yarinyar, sannan ya bukaci iyayenta da su jure wannan rashi da jajircewa da kuma fawwalawa Allah lamari,”

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *