News
Kungiyar ASUU Reshen Jami’ar KUST Wudil Za ta Tsunduma Yajin Aiki
Daga Yasir sani Abdullah
Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU reshen jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil ta shirya shiga yajin aiki daga yanzu zuwa kowanne lokaci.
Shugaban kungiyar ta ASUU, Malam Muhammad Sani Gaya ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da jaridar Daily News 24 a ranar Juma’a.
Malam Muhammad Gaya ya ce zasu shiga yajin aikin ne saboda rashin biyansu alawus-alawus.
Kungiyar ta ce zasu fara yajin aikin ne da zarar sun samu amincewa daga uwar kungiyar ta kasa.
Advertisements
-
News19 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
