News
YANZU-YANZU: Akwai fargabar fasinjoji sun rasu yayin da jirgin ƙasa ya murƙushe tirela da adaidaita-sahu a Kano
Daga Musa naseer musa
Ana fargabar wasu fasinjoji sun rasa rayukan su yayin da wani jirgin ƙasa da ke tafiya ya murkushe tirelar Siminti ta Dangote da babur mai ƙafa uku, wanda a ke kira da adaidaita-sahu a Jihar Kano.
Lamarin ya faru ne a kan titin Obasanjo a cikin birnin Kano da misalin karfe 11:30 na safiyar yau Lahadi.
Shedun gani da ido da ke gudanar da sana’o’i a kusa da titin jirgin, sun ce sun ga tirelar ta nufo layin dogo ne a lokacin da jirgin shima ya keto a guje.
Shaidu sun ce sun yi ƙoƙarin su tsaida tirelar amma direban bai kula ba, inda ya sharo motar da gudu ba tare da lura cewa jirgin ya kawo kai ba.
“Lokacin da direban tirelar ya yi ƙoƙarin ketare layin dogo, sai kawai jirgin yai ciki da motar. Shi kuma wannan mai adaidaita-sahun, shima yana biye da bayan tirelar, sai jirgin ya haɗa da su duka ya make a lokaci guda,” in ji ɗaya daga cikin shaidun gani da ido.
Shaidun sun ce an garzaya da fasinjojin da ke cikin babur din asibiti a halin rai-kokai mutu-kokai, yayin da a ke kyautata zaton direban tirelar ya tsira da ransa.