Connect with us

News

Malam Isa Ali Pantami ya samu kai ziyara Kano gidan su Hanifa Abubakar,

Published

on

FB IMG 16429400532121155
Spread the love

 

Daga kabiru basiru fulatan

 

Advertisement

 

Malam Isa Ali Pantami ya samu kai ziyara Kano gidan su Hanifa Abubakar, yarinya ‘yar shekara biyar wanda aka kama shugaban makarantarsu kan laifin kisan ta.

Farfesa Pantami ya yi ta’aziyya ga mahaifin yarinya, Malam Abubakar, sannan mahaifin yarinyar ya jagoranci shiga cikin gida in da ya yi ma mahaifiyar da yan’uwanta ta’aziyya da nasihohi.

Advertisement

Malam Ya yi nasiha ga iyayen yarinya mai albarka, akan wajibcin hakuri lokacin jarrabawa mai tsanani irin wannan. Farfesa Pantami, ya roki Allah Ya sanya Marigayiya Hanifa Abubakar ta zama mai ceto a lahira ga iyayenta, Ya kuma bawa iyayen hakuri akan wannan babban rashi da ya faru sanadiyar wasu azzalumai da suka nuna rashin imani.

Iyayen sun yi godiya ga Malam da adduar fatan alheri akan nasihohi da addu’o’i da ya gabatar.

Allah Ya kiyaye na gaba.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *