Annobar korona ta sa an fasa auren Firaiministar New Zealand, kuma sai nan gaba za a sanar da sabon lokacin da za a yi auren.
New Zealand ta sanya dokar takaita taruwar jama’a na kar su haura mutum 9, bayan samun wadanda suka kamu da cutar koronba nau’in Omicron a wani gidan biki.
Fira Minista Jacinda Ardern, ta ce daga tsakar daren ranar Lahadi, dokar taruwar mutane 100 a wajen biki amma wadanda suka yi rigakafin korona za ta fara aikin, ya yin da wadanda ba su yi rigakafin ba ba za su haura mutum 25 ba.
Mis Ardern tabbatar da cewa saboda halin da ake ciki ita kan ta an dage lokacin aurenta.
Mutum 9, iyalan gida guda aka gano sun kamu da nau’in Omicron, wadanda suka taso daga Auckland domin halartar biki a New Zealand din.