Kocin ƙwallon ƙafa na tawagar Super Eagles ta Najeriya, Austin Eguavoen, ya ajiye aiki a matsayin kocin riko bayan an fitar da kungiyar daga gasar Kofin Ƙasashen Afrika ranar Lahadi.
Bayan nasarorin da suka samu a wasannin rukuni, kungiyar ta kasa yin nasara a kan Tunisiya a wasan zagaye na ‘yan 16.
A wani taron manema labarai wanda aka yi bayan wasan, Eguavoen ya ce ya yanke hukuncin komawa tsohon matsiyansa na mai kula da harkokin wasanni na NFF.
Advertisement
Eguavoen ya ce “abin da zai faru shi ne; ni ne kocin riko kuma mai kula da harkokin wasanni na NFF, zan koma matsayina kuma zan bar wa hukuma zabi na abin da zai faru a gaba”.
Da ma dai tuni Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta ɗauki sabon koci dan kasar Portugal, Jose Peseiro.
Najeriya ta yi rashin nasara ne a wasan da ci 1-0 bayan Youssef Msakni ya cilla ƙwallo a ragar ta Super Eagles a minti na 47.