Gabannin karawar da Ƙungiyar Super Eagles ta Najeriya za ta yi da Tunisia a yau a Kamaru a gasar cin kofin Afrika, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tattaunawa ta bidiyo da ƴan wasan na Super Eagles.
A wani saƙo da Shugaban ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya buƙaci ƴan wasan da su ci gaba da sa ƴan Najeriya farin ciki inda ya ce kada su tsaya a cin wannan wasa na yau kaɗai, su ɗauki kofin baki ɗaya.
Shugaban ya yi magana da kocin Najeriya Augustine Eguavoen da Keftin ɗin ƙungiyar Ahmed Musa da Amaju Pinnick wanda shi ne Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya da jakadan Najeriya a Kamaru Janar Abayomi Olanishakin mai ritaya.
Shugaban ya gode wa kocin Najeriya da sauran muƙarrabansa kan irin jajircewar da suke yi wajen ganin an samu nasara.