News
An rantsar da mai shari’a mace a karo na farko a Pakistan
Daga Yasir sani Abdullah
A karo na farko an rantsar da mai shari’a a Kotun Kolin Pakistan a babban birnin kasar Islamabad.
Ayesha Malik, mai shekara 55, yanzu za ta rinka zama tare da sauran alkalai maza 16 a babbar kotun kasar mai rinjayen Musulmi.
Lauyoyi da masu raji sun bayyana nadin da cewa wata nasara ce ta daban bayan gwagwarmaya ta gomman shekaru ta ganin an samu wakilcin mata a kasar ta Pakistan wadda maza suka mamaye kusan komai.
Sai dai wasu lauyoyin da alkalai sun soki nadin Ayesha saboda ba ta kai wasu daga cikin ‘yan takarar mukamin ba a matsayi.
Kungiyar kare hakkin dan-Adam ta Human Rights Watch ta ce Pakistan ce kasar Asia daya da ba a taba nada wata mace a matsayin mai shari’a a Kotun Koli ba.
Haka kuma kashi hudu cikin dari ne kawai na alkalan kasar mata.
Ayesha wadda ta yi karatu a kwalejin koyon aikin lauya ta Pakistan da Jami’ar Harvard ta Amurka, ta yi aiki a a matsayin babbar mai shari’a a birnin Lahore da gabashin Pakistan tsawon shekara 20.
Ana ganin ta taka rawa sosai wajen kalubalantar shari’o’i da maza ke danniya a lardin.