News
Kofin duniya ya matso, Ku karawa Super Eagles kwarin gwiwa – Buhari ga ‘yan Najeriya
Daga kabiru basiru fulatan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da martani kan rashin nasarar da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya ta yi a kasar Tunisia a ranar Lahadi, 23 ga watan Janairu a birnin Garoua na kasar Kamaru.
Shugaban ya ce duk da cewa kungiyar ba ta kai yadda ‘yan Najeriya ke zato ba a gasar #AFCON ba, jami’ai da ‘yan wasa sun cancanci a yaba musu kan gwagwarmayar da suka yi.
Shugaba Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su kara wa ‘yan wasan kwarin gwiwar yin abin da ya dace a karo na gaba, musamman ganin yadda wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da aka shirya musu.