Connect with us

News

Ba zan bata lokaci wajen sanya hannu kan takardar hukuncin kisa ga wanda ya kashe Hanifaa ba — Ganduje

Published

on

FB IMG 16428486365916629
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya yi alkawarin mutunta dokar da kundin tsarin mulki ya tanada a matsayinsa na gwamnan wajen sanya hannu kan hukuncin kisa a irin wannan yanayi, idan kotu ta yanke hukuncin a kan kisan gillar da aka yi wa yarinya ‘yar shekara 5, Hanifa Abubakar.

Ya baiyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya tare da mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna, shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar, Labaran Abdul Madari da sauran manyan jami’an gwamnati, ga iyayen Hanifa da ke Dakata/Kawaji, a jiya Litinin.

“Muna da kwakkwaran tabbaci daga kotun da za ta yi shari’ar cewa, za a yi adalci,” in ji shi.

Advertisement

Ganduje ya tabbatar da cewa, “Duk wanda aka samu da wannan danyen aiki, shima zai fuskanci kisa ba tare da bata lokaci ba. A matsayinmu na gwamnati mun riga mun fara shirye-shiryen.”

Gwamna Ganduje ya ce “Tsarin mulkin mu ya tanadi cewa idan aka yanke hukuncin kisa, ikon da tsarin mulki ya bayar shi ne gwamna ya ba da izinin aiwatar da hukuncin kisan. Ina tabbatar muku da haka, ba zan bata ko da dakika daya ba.”

A kan gaggawar gudanar da shari’ar, ya tabbatar da cewa za a gaggauta gudanar da shari’a, inda ya kara da cewa, “gwamnati za ta kula da iyalan marigayiya kuma ƴar mu Hanifa mai albarka.”

Advertisement

Ga makarantun da wannan bala’i ya shafa, Gwamna Ganduje ya bayyana cewa, gwamnati za ta yi wani abu a kan makarantun.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *