News
An sako mahaifiyar ɗan majalisa bayan an biya kuɗin fansa
Daga Muhammad zahraddin
Masu garkuwa da mutane sun sako mahaifiyar shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano Isyaku Ali Ɗanja.
Ɗan majalisar ne ya tabbatarwa da Freedom Radio hakan da safiyar Talata.
Ya ce, an same ta a garin Gumel na jihar Jigawa kuma yanzu haka suna kan hanya domin ɗaukota.
Wasu rahotanni sun ce kafin sakinta dai da aka biya kuɗin fansa kimanin Naira Miliyan Arba’in.
A ranar 12 ga watan Janairun da muke ciki ne, ƴan bindiga suka kutsa kai kai har cikin gidanta a garin Ɗanja na ƙaramar hukumar Gezawa, inda suka yi awon gaba da ita