News
An sanya ranar fara rijistar jarrabawar JAMB ta 2022
Daga kabiru basiru fulatan
Hukumar shirya jarrabawa shiga manyan makarantu ta ƙasa (JAMB) ta sanya ranar da za a fara rijistar jarrabawar.
Kakakin hukumar mai suna Dr Fabian Benjamin, ya ce za a fara rijistar ne a ranar 12 ga Fabarairu zuwa 19 ga Maris na 2022.
Hukumar ta sanar da wannan ne ta takardun sanarwa da take fitarwa, na ranar Litinin 24 ga Janairun wannan shekarar.