News
Babu abin da ya sauya a yaƙi da cin hanci a Najeriya a 2021 – Rahoto
Daga muhammad muhammad zahraddin
Wani rahoto kan cin hanci da rashawa da ƙungiyar CISLAC ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Transparency International (TI) suka fitar ya ce har yanzu babu wani sauyi da aka samu a Najeriya game da yaƙi da cin hanci da rashawa.
Kungiyoyi daban-daban ne suka tattara bayanai kan matsalar cin hancin a duniya, inda TI ta saka Najeriya a matsayi na 154 cikin ƙasashe 180 a shekarar 2021.
Sabon rahoton ya ce Najeriya ta samu maki 24 ne kacal daga cikin 100 da ya kamata a ce ƙasa ta samu don tsira daga matsalar rashawa.
Matsalar ta kara ƙazancewa a Najeriya ne idan aka kwatanta da alƙalumman shekarar 2020, inda ta samu maki 23 cikin 100.
Ƙasashe maƙota kamar Nijar (31) da Kamaru (27) da Chadi (20) na gaban Najeriya a matsayin waɗanda ke da sauƙin matsalar rashawa.
“Wannan abin baƙin ciki ne; a Najeriya aiki ba za ka samu ba sai ka biya cin hanci, makaranta sai an biya cin hanci, samun shaidar tuƙi sai an biya cin hanci, kai har asibiti ma sai mutum ya biya cin hanci,” a cewar Auwal Musa Rafsanjani, shugaban CISLAC kuma wakilin Transparency International a Najeriya.
Rahoton ya yaba wa hukumar EFCC, wadda ya ce ta samu ci gaba a wajen tabbatar da hukuncin kotu a kan mutane da yawa. Kazalika, ya yaba wa hukumar wajen kama masu zamba ta intanet.
Ƙungiyoyi da hukumomin bincike takwas ne suka gudanar da binciken.
Ita ma Hadiza Sani Kan Giwa, ɗaya daga cikin waɗanda suka gudanaar da binciken a CISLAC, ta ce matsalar cin hanci da rashawa a Najeriya na yi wa muhimman ɓangarori mummunar illa.
Ƙungiyar ta ce nan gaba kadan za ta miƙa rahoton ga hukumomin Najeriya, tana mai fatan gwamnatin za ta ɗauki matakan da suka dace don yaƙar da rashawa.
Rahoton na TI ya lissafa wasu sashe bakwai da ya ce su ne ɓangarorin da gwamnatoci a Najeriya suka gaza a yaƙi da cin hanci da rashawa.
“Waɗan nan abubuwa ne suke bayyana dalilan da ya sa Najeriya ta samu koma-baya a yaƙi da cin hanci kuma su ne ke buƙatar ayyukan gaggawa don inganta rayuwar ‘yan Najeriya da tattalin arziki,” in ji rahoton.
Jerin abubuwan da TI ta lissafa su ne:
- Gaza aiwatar da shawarwarin rahoton da ofishin babban akanta na ƙasa ya fitar a Nuwamban 2021
- Rashawa a sashen tsaro na ƙasar
- Gazawa wajen bincika rashawa da wasu manyan ‘yan siyasa suka aikata, “musamman waɗanda suka sauya jam’iyya”
- Rashin bayyana kadarorin da aka ƙwato ƙarara da kuma kare masu kwarmata bayanai
- Matsaloli a ɓangaren shari’a
- Toshe dandalin sada zumunta na Twitter da aka yi “wanda ke tauye haƙƙin ‘yan ƙasa na faɗar albarkacin baki”
Rahoton na Transparency International ya nuna cewa ƙasa mafi girman matsalar cin hanci a nahiyar Afirka a 2021 ita ce Tsibirin Seychelles da ke da maki 70.
A gefe guda kuma, Sudan ta Kudu ce mai mafi ƙanƙantar matsalar, inda ta samu maki 11.
Jumilla, ƙasashen Afirka da ke cikin ƙungiyar Haɗin Kan Afirka ta African Union sun samu maki 33 cikin 100.