Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta kwace kwalaben giya 1,906 a sumamen da ta kai a lokuta daban-daban a fadin jihar a shekarar da ta gabata, 2021.
Kwamandan rundunar, Mallam Ibrahim Dahiru, shi ne ya sheda wa kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, a Dutse, babban birnin jihar, a ranar Talata, 25 ga watan Janairun 2022.
Mallam Ibrahim ya ce sun yi nasarar kwace giyar ne a otal-otal da wuraren shan barasa daban-daban a fadin jihar.
Shugaban Hisbar ya kuma ce sun kama mutum 92 da suke zargi da aikata laifuka na badala daban-daban, wadanda suka hada da karuwai a lokacin sumamen nasu.
Laifukan da ake zargin mutanen sun aikata sun hada da caca da yawan-ta-zubar da shirya liyafar casu a lokacin biki da sauransu, in ji kwamandan.
Haka kuma ya ce a tsawon lokacin hukumar ta Hisbah ta rufe gidajen karuwai.
Mallam Ibrahim ya kara da cewa an mika kwalaben giyar da aka kwace da mutanen da aka kama ga ‘yan sanda domin kara bincike.